• English
  • Business News
Sunday, November 2, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masar Ta Kaddamar Da Shirin Koyar Da Sinanci Na Gwaji A Makarantun Midil Na Kasar

by CMG Hausa
3 years ago

LABARAI MASU NASABA

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

A jiya ne, aka shirya wani biki a kwalejin Confucius na jami’ar Alkahira dake kasar Masar, don kaddamar da wani shirin koyar da harshen Sinanci na gwaji a makarantun midil da kuma shirin horar da malaman kasar.

Jami’i mai kula da harkokin ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Masar Zhang Tao, ya bayyana a cikin wani sakon bidiyo cewa, makarantun sakandaren gwamnatin Masar guda 12 ne za su shiga cikin shirin na gwaji, abin da ke zama wani sabon mafari na koyar da harshen Sinanci a makarantun midil na kasar.

  • Kasashen Sin Da Togo Sun Samu Sakamako Mai Kyau A Fannin Hadin Gwiwa

Zhang ya bayyana cewa, a watan Satumba na shekarar 2020 ne, kasashen Sin da Masar suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna, don koyar da harshen Sinanci a matsayin harshen waje na biyu na zabi a makarantun firamare da sakandare na Masar.
Ya kara da cewa, kasashen biyu sun kuma samu babban ci gaba a fannin hadin gwiwar makarantu, da koyar da sana’o’i, da hazikai, da kuma hadin gwiwa a fannin binciken kimiyya.
A nasa bangaren, mataimakin ministan ilimi da ilimin fasaha na Masar Mohamed Megahed, ya bayyana cewa, a ’yan shekarun nan, kasashen Masar da Sin sun karfafa hadin gwiwarsu a fannin ilimi.
Ya kara da cewa, an yi nasarar kaddamar da shirin koyar da Sinanci na gwaji ne, shekara guda kafin lokacin da aka tsara, sakamakon kokarin hadin gwiwa da bangarorin biyu suka yi, yana mai fatan shirin zai taimaka wa Masirawa da dama kara fahimtar kasar Sin.
Shirin horar da malaman, zai dauki tsawon kwanaki 10, inda za a koyar da darussa game da hanyoyin koyarwa, da koyan harshe, da yadda za a yi amfani da ma sarrafa littattafai na yanar gizo. Malamai 12 ne za su fara aikin koyar da harshen Sinanci bayan kammala samun horon. (Mai fassara: Ibrahim Yaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
Daga Birnin Sin

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

November 1, 2025
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

November 1, 2025
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Daga Birnin Sin

Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

November 1, 2025
Next Post
Adadin Kudin Shigar Kayayyakin Manhajar Masana’antun Sin A Watanni 7 Na Farkon Bana Ya Karu Da Kaso 8.7 Bisa Dari

Adadin Kudin Shigar Kayayyakin Manhajar Masana’antun Sin A Watanni 7 Na Farkon Bana Ya Karu Da Kaso 8.7 Bisa Dari

LABARAI MASU NASABA

Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci

Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci

November 2, 2025
Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

November 1, 2025
Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

November 1, 2025
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

November 1, 2025
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

November 1, 2025
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

November 1, 2025
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

November 1, 2025
Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar

November 1, 2025
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 1, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.