Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutane shida da suka hada da ‘yan sanda uku a wani hadarin da ya faru a ranar Talata a kan hanyar Argungu zuwa Birnin Kebbi a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abubakar Nafi’u ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Birnin Kebbi.
“Hatsarin ya faru ne a lokacin da wata mota kirar Carina E dauke da jarkokin Man fetur, da ake zargin wasu jami’an hukumar kwastam ne daga Birnin Kebbi suke binta.
“Lokacin da ta isa kauyen Jeda, motar Carina E ta yi karo da motar ‘yansanda, sakamakon haka, ta kama da wuta tare da cinye motoci biyar da babur daya kurmus.
“Mutane shidan da suka rasu, sun hada da jami’an ‘yan sanda uku da farar hula uku a gobarar yayin da wasu mutane biyar da ‘yan sanda uku suka samu raunuka daban-daban amma an garzaya da su Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Birnin Kebbi domin kula da lafiyarsu,” inji shi.
Nafi’u ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Ahmed Magaji-Kontagora, ya ziyarci inda hadarin ya faru.