Hukumar kula da ilimin fasaha da Kimiyya ta kasa (NBTE) ta amince da cigaba da wasu Kwasakwasai guda 37 da Kwalejin Kimiyya ta gwamnatin tarayya ke gudanarwa ta Bida dake Jihar Neja.
A wata wasika mai dauke da sa hannun daraktan shirye-shiryen hukumar, Ngbede Ogah kuma aka mika wa shugaban kwalejin, takardar amincewar za ta dauki tsawon shekaru biyar bayan haka za a sake bitar takardar amincewar.
Shirye-shiryen da aka amince da su sune: ND Computer Engineering Technology, ND da HND Chemical Engineering Technology, ND da HND Electrical Engineering (Electronic and Telecom da Power and Machines zabin), HND Agric da Bio-Environmental Engineering Technology (Farm Power and Machinery), ND da HND Building Technology, ND da HND Quantity Surveying, da ND da HND Surveying and Geo-informatics.
Sauran sun hada da ND Architectural Technology, ND Urban and Regional Planning, ND Estate Management and Valuation, ND Tourism Management, ND Agric Technology, ND Horticultural Technology, ND Library and Information Science, HND Public Administration, ND da HND Business Administration, ND da HND Office Technology and Management, HND Nutrition and Dietetics, da HND Statistics, ND Science Laboratory Technology da kuma zabi bakwai na HND Science Laboratory Technology.
Da yake mayar da martanin godiya, shugaban kwalejin, Dakta Abubakar Abdul Dzukogi, ya bayyana jin dadinsa kan sakamakon amincewar da aka basu, ya kuma yi alkawarin cigaba da inganta shirye-shiryen da kwalejin ke gudanarwa.