Adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta kashe a Jihar Jigawa da ke arewacin Nijeriya sun kai 108 tun daga watan Agusta.
BBC ta rawaito cewa, Rundunar ‘Yansanda reshen jihar ta ce akasarin mutanen sun rasu ne sakamakon nitsewa a ruwa da tsawa da kuma rushewar gine-gine.
- Ambaliyar Ruwa Ta Yi Ajalin Mutane 50, Da Dama Sun Rasa Muhallansu A Jigawa
- Ɓarnar Ambaliyar Ruwa A Jigawa
Mai magana da yawun rundunar, Lawan Adam, ya bayyana a yau Asabar cewa an tattara adadin ne tun daga watan Agusta.
A gefe guda kuma, Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya nemi gwamnatin tarayya ta ayyana jiharsa a matsayin “wadda bala’i ya afka mata” saboda ambaliyar ruwan da ta fuskanta.