2023: Wajibi ne kafafen yaɗa labarai su yi adalci ga jam’iyyu a lokacin yaķin neman zabe.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta fayyace wa kafafen yaɗa labarai dokoki da ƙa’idojin bai wa jam’iyyun siyasa lokuta daidai da juna a yayin kamfen.
Shugaban hukumar ne, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi masu wannan bayani dalla-dalla, lokacin da ya ke jawabi wajen taron ƙara wa kakafen yaɗa labarai na talbijin da radiyo ilmin sanin makamar yayata jam’iyyun siyasa a yayin kamfen.
An shirya taron ne a cikin makon nan a Abuja, domin ƙara ɗora su kan hanyoyin da doka ta tanadar wajen tabbatar da bin ƙa’ida yayin yaƙin neman zaɓen 2023.
A ranar 28 ga Satumba ce INEC ta amince aka fara kamfen, kamar yadda Sashe na 94 (1) na Dokar Zaɓe ta 2022 ya tanadar.
“Yayin da za a fara yaƙin neman zaɓen 2023, ya na da muhimmanci dukkan jam’iyyu, ‘yan takara, magoya bayan su da kafafen yaɗa labarai su sani cewa, su na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da an gudanar da komai bisa yadda doka ta gindaya.
“Kada a riƙa yayata kalaman ƙiyayya, zage-zage, sakin-baki, kalaman tunzira jama’a ko harzuƙa wani ɗan takara, aibatawa ko muzantawa, cin zarafi, lahanta wani ko lalata kayan kamfen ɗin wata jam’iyya,” inji Yakubu.
“Sashe na 95 na Dokar Zaɓe ta 2022 ya fayyace komai dangane da ƙa’idojin da ba a yarda a karya ba.
“Mun sha samun ƙorafe-ƙorafen hana jam’iyyun adawa samun damar yin amfani da kayayyaki mallakar gwamnati, kamar kafafen yaɗa labarai ko filayen yin kamfen.
“Ina jaddada cewa yin amfani da ƙarfin mulki a hana jam’iyyar adawa dama daidai da jam’iyya mai mulki a kafafen yaɗa labarai na gwamnati, haramun ne a dokar INEC Sashe na 95 (2,3,4,5,6).
“Kafafen yaɗa labarai na gwamnati kada su hana wata jam’iyya damar yayata manufofin ta daidai da lokacin da su ka bai wa jam’iyya mai mulki.”
Yakubu ya ce akwai hukunci da Dokar INEC ta tanadar ga kafar yaɗa labaran, wanda ya haɗa da cin tara ta naira miliyan biyu. “Amma idan aka sake karya dokar, to sai an biya naira miliyan biyar. Shi kuma shugaban kafar yaɗa labarai ko ma’aikatan da su ka karya dokar, za a ci su tara ta naira miliyan ɗaya, ko ɗaurin watanni shida a kurkuku.”