Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata a Abuja, ya ce cin hanci da rashawa a fannin ilimi na ci gaba da durkusar da tallafin gwamnati a manyan makarantu, inda ya bukaci da a dinga sanya idanu kan kudaden da ake warewa bangaren ilimin.
Shugaban wanda ya bayyana hakan a wajen wani taro na kasa karo na 4 kan nemo dabarun rage cin hanci da rashawa a bangaren ma’aikatun gwamnati a fadar gwamnatin tarayya, Abuja, ya bayyana cewa kula da kasafin kudi na bangaren ilimi, ya zama dole a sa ido kan tsarin fitar da kudaden.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya fitar, hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) da ofishin sakataren gwamnatin tarayya (OSGF) da hukumar shirya jarabawar shiga jami’a (JAMB) ne suka shirya taron.