Majalisar kare hakkin bil Adama ta MDD, ta yi watsi da wani daftari da ya shafi jihar Xinjiang, wanda wakilin Sin ya bayyana a matsayin wani yunkuri na amfani da hukumomin kare hakkin dan Adam, domin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Sin, da amfani da batutuwan da suka shafin Xinjiang domin dakile ci gaban kasar.
Chen Xu, shugaban tawagar kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva ne ya bayyana haka, inda ya ce Amurka da wasu kasashe ne suka shirya tare da gabatar da daftarin, suka kuma mika shi a matsayin matsalar dake bukatar gyara, a yunkurinsu na gaskata nazarinsu da ya sabawa doka, da sanya batutuwan da suka shafi Xinjiang da babu su a zahiri, a cikin ajandar majalisar.
Ya bayyana gabanin kada kuri’a a jiya Alhamis, a zama na 51 na majalisar kare hakkin bil Adama cewa, batutuwan da suka shafi Xinjiang, ba su da alaka ko kadan da na hakkokin dan Adam, yana mai cewa, batutuwa ne da suka shafi yaki da ta’addanci da ra’ayi mai tsauri da kuma yaki da ‘yan aware.
Ya kuma shaidawa majalisar cewa, bisa namijin kokarin da aka yi, ba a samu ayyukan ta’addanci a Xinjiang ba, cikin shekaru 5 a jere. Kuma ana ba da cikakkiyar kariya ga hakkokin dukkan kabilun dake jihar.
A cewar Chen Xu, cikin sama da shekaru 60 da suka gabata, yawan al’ummar Uygur na Xinjiang ya karu daga miliyan 2.2, zuwa kusan miliyan 12, kuma matsakaicin shekarunsu na rayuwa ya karu daga 30 zuwa 74.7.
Ya ce ta hanyar yin biris da shaidu da gaskiya, Amurka da sauran wasu kasashe sun shirya tare da yada karairayi da jita-jita, a yunkurinsu na bata sunan Sin da kawo cikas ga zaman lafiya a jihar Xinjiang da dakile ci gaban kasar. Ya ce wannan misali ne na kulli irin na siyasa da take hakkin dan Adam mai tsanani, na dukkan kabilun jihar Xinjiang.
Bugu da kari, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin ya bayyana a jiyan cewa, shaidu sun nuna sau da dama cewa, siyasantar da batun hakkin dan Adam, da nuna fuska biyu, ba za su yi tasiri ba, kuma yunkurin amfani da batutuwan da suka shafi jihar Xinjiang domin durkusarwa ko dakile kasar Sin ba zai yi nasara ba. (Fa’iza Msutapha)