Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, ya rushe shugabannin kananan hukumomi 20 da dukkanin kansilolin jihar baki daya.
Wannan matakin ya biyo bayan karewar wa’adin mulkinsu na shekara biyu bayan da aka zabesu a 2020.
- Asirin Barawon Da Ake Zargin Ya Sace Kudin Da Ake Tarawa A Coci Ya Tonu
- Shin Gwamnatin Birtaniya Ta Saurari Kiran Kungiyar OAS Kan Tsibiran Malvinas
A wata sanarwar da kakakin gwamnan, Mukhtar Mohammed Gidado, ya fitar a daren ranar Asabar, gwamnan bisa dogaro da sashen dokar ta 2 (I) na tsarin kananan hukumomi ta Jihar Bauchi na 2013, wa’adin zababbun shugabannin kananan hukumomin da mataimakansu hadi da kansilolin jihar zai kare ne daga ranar 10 ga watan Oktoban 2022.
Sanarwar ta umarci shugabannin kananan hukumomin, mataimakansu da kansiloli da su mika ragamar shugabanci ga manyan jami’an kananan hukumomin nasu a ranar Talata 11 ga watan Oktaban 2022 kafin zuwa lokacin da za a gudanar da sabon zabe ko kuma nada kantomomin rikon kwarya.
Daga bisani gwamna Bala Muhammad ya gode tare da jinjina wa shugabannin da mataimakansu hadi da kansilolin a bisa kokarinsu da aiki tukuru da suka gudanar domin ci gaban yankunan da suka mulka, ya musu fatan alkairi a rayuwarsu na gaba.
Wakilinmu ya nakalto cewa shugabannin kananan hukumomin jihar sun shafe shekaru biyu a bisa karagar mulki kamar yadda doka ya tanadar.