Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta gabatar da gudummawar da kasar Sin ta bayar ga bunkasar tattalin arzikin duniya a cikin shekaru 10 da suka gabata, yayin wani taron manema labarai da aka saba gudanarwa Lahadin nan, inda ta bayyana cewa, kasar Sin za ta kara ba da gudummawa wajen samun ci gaban tattalin arzikin duniya mai karfi, dorewa, daidaito da wanda zai shafi kowa da kowa. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)