Galibi ana kafa asusu ne da nufin inganta fannoni na ilimi ko harkokin ci gaban mata da kananan yara ko raya harkar lafiya da agazawa wadanda bala’o’i suka shafa da makamantansu.
Kamar sauran irin wadannan asusu da kasashe ko al’ummomi ko kungiyoyi masu zaman kansu ke kafawa, shi ma asusun raya yankunan karkara na kasar Sin ko CFRD a takaice, ya amsa manufofin kafa shi, duba da irin managartan ayyukan da yake gudanarwa a ciki da wajen kasar.
Ayyuka na baya-bayan da asusun ya gudanar a kasar Habasha, ya samu yabo da jinjina, a daidai lokacin da aka yi bikin cikarsa shekaru 3 da bude ofishinsa a kasar ta Habasha.
Shi dai asusun ya fara gudanar da ayyuka daban daban a Habasha tun daga shekarar 2015, an kuma yi masa rajistar gudanar da ayyuka a matsayin asusun ba da tallafin jin kai na kasa da kasa a kasar a watan Yulin shekarar 2019, inda ya karkata ga zurfafa hadin gwiwar musaya tsakanin al’ummun Sin da na kasar Habasha.
Bayanai na nuna cewa, asusun CFRD ya shafe shekaru 7 yana gudanar da ayyuka daban daban a Habasha, ciki har da ciyar da daliban makarantu, da raba kayan karatu, da kayan abinci, da ruwan sha da ayyukan tsaftar muhalli, da ayyukan bunkasa tattalin arzikin mata, ayyukan da suka amfani sama da ’yan kasar Habashan 250,000.
Hakika ayyukan asusun CFRD, sun yi daidai da muhimman ayyukan da gwamnati da al’ummun Habasha ke bukata, wadanda ke da matukar tasiri ga ci gaban kasar.
Sabanin yadda wasu kasashen yammacin duniya ke kafa asusu da sunan raya demokiradiya ko Ilimi ko wasu bangarori na rayuwa, amma suke fakewa da hakan wajen tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashe da ma neman shafa musu bakin fenti ko hana ci gabansu.
Wannan ne ma ya sa babban daraktan kungiyoyi masu zaman kansu na kasar Habasha Jima Dilboi ya yi kira ga asusun na CFRD, da ya jagoranci kungiyoyi masu zaman kansu dake Habasha, wajen kulla alaka da sauran kungiyoyi da hukumomi na kasa da kasa, kamar shirin samar da ci gaba na kasa da kasa, da na hadin gwiwar bunkasa kasashe masu tasowa, da shirin ziri daya da hanya daya. A daina fakewa da guzuma ana harbin karsana. (Ibrahim Yaya)