Shugaban kungiyar Miyeti Allah reshen jihar Filato, Muhammed Nuru, ya yi ikirarin cewa, kimanin ‘ya’yan kungiyar 20 ne masu garkuwar suka sace a jihar a cikin mako guda.
Nuru, wanda ya sanar da hakan a garin Jos, ya bayyana nawa, yanzu fulani makiyaya a jihar na cikin tsoro saboda sace su da masu garkuwar ke yi, inda ya kara da cewa, garkuwar har ta janyo suna jin tsoron fita da dabbobi su yin kiwo.
- Tun A 2003 ‘Yan Fansho Ke Bin Gwamnatin Kano Bashin Naira Billiyan 69 – NLC
- Sayen Kuri’u Zai Mamaye Zaben 2023 –Dakta Hakeem
‘Ya’yan kungiyar a jihar na fuskantar barazana a garin Jos da Jos ta Yamma da kuma kananan hukumomin Bokkos da Waseda.
Nuru ya ce, bisa kokarin jami’an tsaro a jihar an samu nasarar kwato kimanin Shanu 500 na ‘ya’yan kungiyar da aka sace, inda aka mayar da su ga masu su a karamar hukumar Wase.
Shugaban ya kara da cewa, jami’an sun kwato Shanun ne a karamar hukumar Biu da ke a jihar Borno, inda kuma aka kwato wasu Shanun a yankin Gwujuba da ke a cikin jihar Yobe.
Shugaban ya ce, ‘ya’yan kungiyar da dama sun kaurace wa karamar hukumar Wase saboda barazanar da suke fusknata ta rayuwarsu, musamman a yankunan Dogoruwa, Kimbi, Penau da kuma Kampani-Zurak.
Nuru ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin jihar Filato da su taimaka domin a kubutar da ‘ya’yan kungiyar da masu garkuwar suka sace
Kakakin Rundunar ‘yansanda da ke garin Jos, DSP Alfred Alabo, ya bayyana cewa, rundunar ba ta samu rahoton yin garkuwa da fulani makiyayan ba.