Jami’an kasashe daban daban sun yaba wa jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), yayin zantawa da wakilan CMG a kwanan baya.
A cewarsu, karkashin jagorancin JKS, jama’ar kasar Sin za su cika babban burinsu na raya kasa, da samar da gudunmowa ga kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya.
A nasa bangare, tsohon ma’ajin jam’iyyar APC ta kasar Najeriya, Adamu Fanda, ya ce JKS ta dukufa wajen raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama’a a kasar Sin, abin da ke nuna cikakkiyar kwarewarta a fannin gudanar da mulki, da samun goyon baya daga al’ummar kasar.
A cewarsa, ya kamata jam’iyyun siyasa daban daban na kasashen Afirka su koyi dabarun JKS, da mayar da hankali kan tabbatar da kwanciyar hankali, da raya tattalin arziki, don amfanawa jama’a.
Ban da wannan kuma, Johnstone Muthama, shugaban jam’iyyar UDA mai mulki a kasar Kenya, ya ce kasar Sin ta ba da dimbin taimako ga kasar Kenya a shekarun nan, musamman ma a fannin raya kayayyakin more rayuwa. Don haka, jam’iyyar UDA na son yin hadin gwiwa tare da JKS don musayar fasahohi, da karfafa mu’ammala, da kara kyautata huldar dake tsakanin bangarorin 2, a kokarinsu na zabar tafarkin raya kasa na kansu, in ji jami’in na kasar Kenya. (Bello Wang)