Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ekiti, Rt. Hon. Funminiyi Afuye, ya mutu yana da shekara 66 a duniya, sakamakon kamuwa da bugun zuciya.
A cewar wata sanarwar da aka fitar daga fadar Gwamnatin jihar Ekiti, Afuye ya mutu ne a ranar Laraba da yammaci a asibitin koyarwa ta jami’ar Ekiti (EKSUTH) da ke Ado-Ekiti, sa’ilin da ke amsar kulawar Likitoci bayan samun bugun zuciya da ya yi.
Sanarwar cikin juyayi dauke da sanya hannun babban sakataren watsa labarai na gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, Yinka Oyebode, ya ce, gwamnati na bakin cikin sanar da mutuwar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar.
“Marigayi Afuye, mai shekara 66, tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Eikiti kuma sau biyu ya zama mambar Majalisar Dokokin jihar. Ya zama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar ne a ranar 6 ga watan June na 2019,” a cewar Oyebode.
Sanarwar ta mika alhini da jimamin wannan babban rashin da iyalai da jihar suka yi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp