A yayin bude babban taro karo na 20 na wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, babban darektan jam’iyyar Xi Jinping ya bayyana a cikin rahoton da ya gabatar cewa, Sin na tsayawa tsayin daka kan manufofin wanzar da zaman lafiya da sa kaimi ga samun bunkasuwa tare, da kuma dukufa kan gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama. Ra’ayin dake jawo hankalin al’ummar duniya sosai.
Manazarta na ganin cewa, rahoton da Xi Jinping ya bayar ya bayyana anniya da kwarin gwiwar Sin na nacewa ga bin hanyar zamanintar da kanta da samun bunkasuwa cikin lumana, JKS za ta ci gaba da ba da babbar gudummawa ga zaman lafiya da ci gaba da wadata a duniya.
Ma’anar hanyar samun bunkasuwa cikin lumana ita ce, samun bunkasuwa tare da kiyaye zaman lafiyar duniya, ta yadda kuma ci gaban da ake samu zai ba da gudunmawa wajen kiyaye zaman lafiyar duniya. (Amina Xu)