A karshen wannan makon ne, aka kammala babban taron wakilan JKS na 20,bayan shafe kwanaki bakwai ana tattauna.
Bayan kammala taron ne kuma babban sakataren kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci sauran shugabannin don ganawa da manema labarai na cikin gida da na waje, inda ya bayyana sabuwar alkiblar da kasar ta dosa, da yadda duniya za ta amfana daga jerin matakan da aka tsara aiwatarwa.
Kamar yadda kasar Sin ta sha bayyanawa, a wannan karon ma, babban sakatare Xi ya kara nanata kudirin kasar Sin na samar da gudummawa ga sauran kasashen duniya wajen samun ci gaba, kuma bunkasuwar kasar Sin za ta yi tasiri ga duniya baki daya. A gabar da kasar ta kama hanyar zamanantar da kanta.
Babban taron wata hanya ce ta kara daga tutar JKS, da hada karfi da karfe, da inganta hadin kai da sadaukarwa, don kara yiwa jama’a hidima da ma dogara da jama’a, da ci gaba da yin gyare-gyaren da suka dace da sabon tafarkin da aka sanya a gaba, sabanin yadda wasu jam’iyyun siyasa a kasashen yamma ke kara cusa jama’arsu cikin halin kunci, sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da yaduwar annobar COVID-19 da nuna wariya da sauransu.
Batun kara bude kofarta ga kasashen ketare, da sa kaimi ga zurfafa yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga waje a dukkan fannoni, bai sauya ba.
Kuma ana iya ganin sakamakon haka, daga alkaluman da hukuma ta fitar dake nuna cewa, cinikayyar kayayyaki na ketare na kasar Sin, a cikin watanni 9 na farkon shekarar 2022 da muke ciki, ya karu da kashi 9.9 cikin 100, zuwa kudin Sin RMB Yuan triliyan 31.11, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 4.75.
A cikin wannan wa’adi, cinikayyar kasar Sin da kasashen dake aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, ya karu da kashi 20.7 cikin 100 kan makamancin lokaci na bara, zuwa Yuan triliyan 10.04.
Wannan yana kara tabbatar da cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da juriya da kuma dama mai kyau, kuma tushen sa mai karfi ba zai taba sauyawa ba, zai kuma ci gaba da kasancewa bisa yanayi mai kyau da inganci na dogon lokaci.
Don haka, kasar Sin mai wadata, za ta kara samar da damammaki ga duniya baki daya. Kuma kamar yadda kasar Sin ba za ta iya samun ci gaba ita kadai ba, haka ma duniya tana bukatar kasar Sin wajen samun bunkasuwarta.
Masana daga sassan daban-daban na nahiyar Afirka wadanda ke zama kawaye kuma aminan kasar Sin, su ma sun bayyana cewa, taron yana da babbar ma’ana, wanda zai haifar da babban tasiri ga kasar Sin, da kara kuzari ga kasashen duniya wajen yin hadin gwiwa don tinkarar kalubale da samun bunkasuwa tare.
Nasarorin da kasar Sin ta cimma a aikin zamanintar da kanta bisa tsarinta, sun karfafa gwiwar kasashen duniya musamman ma kasashe masu tasowa, wannan zai baiwa sauran kasashe masu tasowa damar zabar dabarun raya kasashensu dake dacewa da yanayinsu. Kowa ne tsuntsu dai kukan gidansu ya ke yi.
Masu fashin baki na fatan kasashen duniya za su koyi fasahohi da shirye-shiryen samun ci gaba na kasar Sin da kuma damar hadin gwiwa daga taron wakilan JKS karo na 20, ta yadda za a tafiyar da harkokin duniya da ma tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta tare. (Ibrahim Yaya)