Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da jakadan kasar Amurka dake kasar Sin, Nicholas Burns, a jiya Jumma’a.
Wang Yi, ya yi maraba da Nicholas Burns a matsayin sabon jakadan kasar Amurka a kasar Sin, kana ya bayyana cewa, yanzu an shiga lokaci mai muhimmanci na raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. Kuma kasa da kasa suna fatan ganin an raya dangantakar ta su yadda ya kamata.
Ya kara da cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi nuni da cewa, ya kamata Sin da Amurka su girmama juna, da yin zama tare cikin lumana, da yin hadin gwiwa da samun moriyar juna, wanda shi ne tushen raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Haka kuma, a matsayinsu na manyan kasashe a duniya, Sin da Amurka ba za su iya sauya tsarin juna ba, don haka bai kamata kasar Amurka ta yi amfani da matsayinta na kasa mafi karfi yayin da take mu’amala da Sin ba, kana kada a yi yunkurin hana ci gaban kasar Sin. Bugu da kari, Wang Yi yana fatan jakadan, zai zama gada wajen raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka.
A nasa bangare, Nicholas Burns ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin tana da muhimmanci sosai ga kasashen biyu, har ma ga duk duniya baki daya.
Kuma kasar Amurka tana son kara yin mu’amala da kasar Sin, da daidaita matsalolinsu, da kuma sa kaimi ga hadin gwiwarsu. (Zainab)