Gwamnatin tarayya ta yi watsi da yekuwar kai hare-haren ta’addanci Abuja da jami’an tsaron kasar Amurka suka fitar a kwanan nan, inda ta ce Nijeriya da ‘yan kasarta na cikin aminci (ba sa cikin hadari).
Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (rtd) ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa a ranar Litinin bayan wani taron gaggawa na majalisar tsaro da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kira a fadar shugaban kasa (Villa) da ke Abuja.
Monguno, ya yi jawabi ga manema labarai tare da Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyema, Babban Hafsan Tsaro (CDS), Janar Lucky Irabor, da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufai Abubakar.
A cewar Monguno, firgicin da ya biyo bayan sanarwar ta’addancin da Amurka ta yi wa ‘yan Nijeriya, sam bai kamata ba, sanarwar ta yada cece-kuce da firgici a tsakanin al’umma kan batun da ba shi da tushe.
Ya bukaci ‘yan Nijeriya da mazauna Abuja da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba.
Ya kuma ce rundunonin soji da jami’an tsaro da na leken asiri suna nan suna jajircewa wajen tabbatar da cewa dukkan ‘yan Nijeriya na kowane bangare na kasar yana cikin aminci.