• English
  • Business News
Saturday, November 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ci Gaban Kasar Sin, Nasara Ce Ta Duniya Ba Kalubale Ba

by CMG Hausa
3 years ago
Kasar Sin

Lamuran da suka faru a duniya, sun nuna mana cewa, nasara da ci gaban duniya, sun dogara ne da hadin gwiwa da taimakekeniya da kuma moriyar juna tsakanin kasa da kasa. Don haka, kyashi ko adawa da ci gaban wata kasa, ba zai taba amfanawa duniya ba.

Yadda kasashen yammacin duniya ke alakanta kasar Sin da kalmar “barazana” ko “kalubale”, abun damuwa ne ga zaman lafiya da ci gaban duniya. Nasarar Sin, nasara ce ga daukacin duniya, bisa la’akari da yadda karuwar tattalin arzikinta ko nasarori ko fasahohi ko ci gabanta ke shafar duniya baki daya.

  • Tashar Sararin Samaniyar Sin Za Ta Kasance “Gida Cikin Sararin Samaniya” Ga Dukkanin Bil Adama

Yayin da suke tattaunawa a makon da ya gabata, sabon Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak da shugaban Amurka Joe Biden, sun bayyana cewa, za su hada hannu wajen magance “kalubalen kasar Sin”.

Shi ma sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg, ya bayyana kasar Sin a matsayin barazana, yayin da yake neman Amurka ta kara taimakawa Ukraine a rikicinsu da Rasha.

Ba mu taba jin inda aka ce kasar Sin ta kitsa juyin mulki a wata kasa ba, haka ma ba mu taba jin cewa Sin ta yi mulkin mallaka ko ci da gumin wasu kasashe ba. Kasar Sin ba ta taba girke sojojinta a wata kasa da sunan kare kanta ba, har ila yau, ba mu taba jin inda aka ce ta yi kutse ko katsalandan cikin harkokin wata kasa ko cusawa wata kasa manufofinta ba.

LABARAI MASU NASABA

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

To ya aka yi ta zama barazana ko kalubale?
Ko kadan, bai kyautu wadannan shugabanni su rika ayyana Sin a matsayin barazana ba, domin hakan, bata suna ne, suna nema jan Sin cikin rikicin da su ne suka rura wutar ta. Neman dorawa Sin laifi, ba zai kawar da hankalin duniya daga ainihin wadanda ke da alhakin haifar da rikicin ba. Kasar Sin ba ta taba sauya matsayarta game da batun Rasha da Ukraine ba, wadda ita ce hawa teburin sulhu.

A ganina, yadda ake alakanta ta da barazana ko kalubale, ba komai ba ne face adawa da ci gabanta da nasarori da farin jininta a idon duniya, wanda kuma ta same su ne ta sahihiyar hanya.

Don haka, yunkurin shafa mata kashin kaji, ba zai haifar da komai ba illa bayyana ainihin masu laifi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Daga Birnin Sin

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

October 31, 2025
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
Daga Birnin Sin

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

October 31, 2025
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
Daga Birnin Sin

Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

October 31, 2025
Next Post
Kumbon Dakin Gwaji Na Mengtian Ya Hade Da Tashar Binciken Sararin Samaniya Ta Kasar Sin

Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa

Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari

October 31, 2025
Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano

An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano

October 31, 2025
Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

October 31, 2025
Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 

Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 

October 31, 2025
Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba

Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba

October 31, 2025
Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar

Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar

October 31, 2025
Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi

Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi

October 31, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.