Mai magana da yawun majalisar dokokin kasar Sin ya bayyana adawa da kakkausar murya kan wani sabon kuduri da majalisar Turai ta amince da shi, kan halin da ake ciki game da batun kare hakkin dan-Adam a jihar Xinjiang.
Kakakin kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin You Wenze ya bayyana cewa, kasar Sin tana adawa da magudin siyasa da tsoma baki a harkokin cikin gidan ta da majalisar Turai ke yi, ta hanyar fakewa da batun kare hakkin bil-Adama.
Manufar yunkurin da wasu makiya kasar Sin dake cikin majalisar dokokin Turai ke yi na neman yin batanci da shafawa manufar kasar Sin kan yankin Xinjiang bakin fenti, ita ce haifar da rashin jituwa tsakanin kabilu daban-daban na kasar Sin, da neman zubar da kimar kasar Sin, tare da dakile ci gabanta. You ya kara da cewa, duk irin wadannan ayyuka ba za su taba yin nasara ba.
You ya bayyana cewa, batutuwan da suka shafi jihar Xinjiang na kasar Sin ba batun kare hakkin dan-Adam, kabilanci ko addini ba ne, amma batun yaki da ta’addanci ne da kuma masu neman ballewa.