Da maraicen yau Alhamis ne Sashen Hausa na Rediyon BBC ya gudanar da bikin karrama waɗanda suka zama gwaraza a gasar waƙoƙin cikar sashen shekara 65 da kafuwa da kuma gasar rubutun zube ta Hikayata.
An karrama waɗanda suka yi rawar gani wajen lashe gasar a bainar dandazon jama’ar da ta taru a Cibiyar Shehu Musa ‘Yar’aduwa da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.
Wanda ya zama gwarzo a gasar waƙar shi ne, Shu’aibu Ibrahim Muhammad inda aka ba shi kyautar Dala 2,000, sai wanda ya zo na biyu, Musa Abubakar da aka ba shi Dala 1,500, kana Zainab A. Baba da ta zo ta uku, ta samu kyautar Dala 1,000.
A ɓangaren gasar Hikayata kuwa, Amira Souley daga Jamhuriyar Nijer ce ta lashe gasar ta 2022 da labarinta mai taken “Garar Biki”, sai Hassana Labaran Ɗanlarabawa da ta zo ta biyu da labarinta mai taken “Haihuwar Guzuma” kana Maryam Muhammad Sani ta zo ta uku da labarinta mai taken “Al’ummata”. Su ma Sashen Hausa na BBC ya ba su daloli irin yadda ya bai wa waɗanda suka lashe gasar waƙa, kowa da matsayinsa da abin da ya samu.
Da yake jawabi, shugaban alƙalan da suka tantance gwarazan gasar waƙar ta cikar BBC Hausa shekara 65 da kafuwa, Farfesa Muhammad Sa’idu Gusau, ya bayyana cewa an gudanar da gasar ce a tsakanin watan Fabarairu zuwa Maris na 2022. Ya ce, wannan shi ne rukuni na farko da aka fara sa waƙa agasar ta BBC, inda aka samu waƙoƙi 301, duk da haka akwai wasu birjik da aka aiko bayan an rufe karɓar waƙoƙin gasar.
Daga cikin waɗanda aka karɓa, an tantance 68 daga cikin 301, daga nan aka sake tantancewa zuwa 32. Har ila yau daga wannan adadin aka sake tantancewa bisa wasu dokokin nazarin waƙa aka fitar da daga ta ɗaya zuwa ta uku, “baya ga ukun nan, an sake tantance wasu 12 waɗanda aka haɗa da waɗanda suka zama gwaraza, sai aka fitar da guda 15. Turken saƙon waƙoƙin shi ne bayyana saƙo a kan ayyukan BBC Hausa a cikin shekara 65. Waƙoƙin sun kawo abubuwa daban-daban kan ayyukan da BBC suka yi.
“BBC za su yaɗa waƙoƙin a shirye-shiryensu, sannan duka gidajen rediyo da suke hulɗa da su da sauran masu sha’awa za a ba su su ci gaba da yaɗawa daga Juma’ar nan ta gobe zuwa illa ma sha Allah.” In ji shi.
Bugu da ƙari, alƙalan gasar waƙoƙain sun gabatar da wasu shawarwari inda suka nemi BBC Hausa ta haɗa da rubutattun waƙoƙi baya ga na baka a gasar. Sun kuma tabbatar da cewa gasar za ta kaifafa basirar masu tsara waƙoƙin da ƙara musu hanyoyin jera tunani da cusa falsafofi a ciki.
Wakazalika sun yi kiran a bai wa maza dama su riƙa shiga gasar Hikayata domin bayar tasu gudunmawar.
Shi ma da yake gabatar da ƙasida game da cikar BBC Hausa shekara 65 da kafuwa, Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, ya yi dogon bayani a kan gudunmawar da BBC Hausa ke bayarwa ga bunƙasa al’adun Hausawa.
Ya rubuta littafi na musamman a kan hakan wanda ya sa wa suna “SANSAMIN GAMJI MAI CIKA BAKIN AKUYA”.
Farfesa Bunza ya bayyana cewa Aminu Abdullahi Malumfashi shi ne mutum na farko da ya fara magana BBC Hausa. Haka nan ya ce akwai gidajen rediyo sama da 400 masu yi wa Hausa hidima a doron ƙasa.
“Cikin harsunan duniya, harshen Hausa shi ne na 11. BBC ta riƙe dukkan jinsin Hausawa da ake da su, kama daga Bahaushe na gidi, da mai barbarar yanyawa da sauransu.”
Ya kwatanta BBC Hausa a matsayin kafar yaɗa labarun da ta yi wa saura fintikau a fagen yaɗa labaru da harshen Hausa, kana ya nemi su ci gaba da jan zarensu.
Shi kuwa mai gabatar da ƙasida ta biyu, Farfesa Umar Alhaji Fate, ya yi bitar cewa shi kansa babban gidan rediyon na BBC mai yaɗa labarunsa da harshen Ingilishi, ya cika shekara 100 da kafuwa a ranar 18 ga Oktobar da ta gabata.
Ya ce yana daga cikin abin da ya sa BBC Hausa ya yi shuhura, kawo wa masu sauraro abubuwan da suke son ji, da ya gabatar da aikin da kuma amfani da kayan aiki na zamani.
Ya yaba wa rediyon a kan yadda yake ƙara harsunan da yake amfani da su a duniya. Har ila yau, ya yi ninƙaya a kan tsarin kafuwar gidan rediyon da yadda yake tafiya da zamani da kuma ‘yanci da yake bai wa ma’aikatansa.
Ya yaba da hanyoyin faɗaɗa sadarwa na zamani da BBC Hausa ke amfani da su da yadda suke tura ma’aikatansu domin binciken ƙwaƙwaf kan wasu al’amura da suka shafi al’umma.
Ya nemi Rediyon ya ci gaba da watsa shirye-shiryensa ta rediyo domin har yanzu akwai waɗanda suke amfani da rediyo ba kafofin sadarwa na zamani ba.
A nata ɓangaren, shugabar alƙalan gasar Hikayata ta bana, Dakta Aishatu Maimota, ta yi tsokaci a kan jigogin labarun da suka yi nasara a gasar tare da bayyana mizanin da suka yi amfani da su wajen tantancewa.
Da take jawabin godiya a madadin waɗanda aka karrama, gwarzuwar gasar Hikayata ta 2022, Amira Souley ta gode wa BBC Hausa a madadin sauran gwarazan, bisa ba su damar gabatar da basirarsu. A cewarta akwai tarin hikimomi da abubuwan da ke damun mata da suke neman kafar da za su amayar, amma sun rasa, shi ya sa suke ƙara jaddada godiyarsu ga BBC Hausa.
Wakazalika, manyan baƙi daban-daban da suka halarci bikin, sun yi jawabai na fatan alheri tare da tuna baya daga wasu tsofaffin ma’aikatan rediyon.
Daga bisani, shugaban BBC na yankin Yammacin Afirka, Ehizojie Okharedia ya taya waɗanda suka lashe gasar murna kana ya tabbatar da cewa za su ci gaba da aiwatar da shirye-shirye masu tasiri ga rayuwar al’umma. Ya gode wa dukkan baƙin da suka halarci bikin bisa amsa gayyatarsu.
Baya ga dalolin da BBC Hausa ya bai wa gwarazan gasar dai, har ila yau, Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna, Farfesa Hafsat Ganduje ta ƙara wa gwarazan daidai adadin yawan dalar da aka ba su, kana Wazirin Katsina ya sake ƙara wa gaba ɗayansu kyautar Dala 1,000 kowanne.