Kungiyar Gwagwarmar Talakawa ta Nijeiya da ke Zariya a Jihar Kaduna ta jagorancin taron wayar da kan al’umma maza da mata da ‘yan siyasa da kuma wasu kungiyoyi masu zaman kansu da suke da alaka da ci gaban al’umma domin zaben shekara ta 2023.
Taron da ya gudana a cibiyar matasa da ke Tudun Wadan Zariya, shugabannin kungiyar da ‘yan siyasa da kuma mahalarta taron sun gabatar da jawabai kan matsalolin da ke cikin dimukuradiyyar Nijeriya da kuma yadda mahalarta taron suka yi tsokaci masu yawan gaske, kan yadda talakawa da suke kan gaba wajen zaben gwamnati.
- Alhassan Doguwa Ya Musanta Samun Sabani Tsakaninsa Da Ganduje
- PDP Ta Maka APC A Kotu, Ta Nemi A Kori Shugaban APC Na Kasa Daga Mukaminsa
A cewar mahalarta taron, talaka shi ne kan gaba wajen shan wahala a tsawon mulkin dimukuradiyyar da ake ciki.
Babban jami’in gudanarwa na kungiyar, Kwamared Tukur Mu’azu, wanda aka fi sani da Tukur Dan Mu’azu ya nunar da cewar sun kafa wannan kungiyar ce domin daukar duk matakan da suka gabata na ganin matsalolin da talakan Nijeriya ke ciki a dalilin zaben wasu ‘yan siyasa da aka yi masu kyakkyawar zaton za su sami mafita daga wasu matsaloli da suke addabarsu daga shekara ta 2015, amma, a cewar Tukur Dan Mu’azu, talaka ya tsinci kan a filin da na sanin zaben da ya yi.
Shugaban wannan kungiya ta Gwagwarmayar Talakawa a Nijeriya, Alhaji Dan Almajiri ya yi tsokaci na yadda mafiya yawan ‘yan siyasa da aka zaba daga shekara ta 2015, babu abin da suka yi wa talakawa.
Shugaban kungiyar ya ce kan matsalolin da aka cusa al’umma, musamman talajawa a Jihar Kaduna da wasu aka kore su daga ayyukan da suke yi, wasu aka rushe musu rumfuna amma duk babu batu daya da aka cika masu sai ma karin bacin rai.