A tsakiyar makon nan ne kamfanin gine-gine na kasar Sin na CCCC ya kammala ginin hanyar motar kwalta mai tsawon kilomita 56.5, a yankin Oromia na kasar Habasha, wanda ya kunshi gina gadoji 4 masu inganci.
Sakamakon kammalar wannan muhimmin aiki, yanzu haka al’ummun dake yankin Oromia za su samu zarafin safarar albarkatun gona masu yawa da inganci da suke nomawa, da suka hada da Alkama, da barley, da ’ya’yan itatuwa zuwa kasuwannin birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar.
Ko shakka babu irin wadannan ayyuka na samar da ababen more rayuwa, wadanda kamfanonin kasar Sin ke yi a sassa daban daban na nahiyar Afirka na da fa’idar gaske, suna kuma kara tabbatar da aniyar Sin da ma su kansu kasashen Afirka na yin tafiya tare, domin cimma nasarar kafa al’ummar bai daya ta Sin da Afirka mai makomar bai daya.
A yankin Oromia na Habasha, wannan aikin hanya baya ga taimakawa manoma da yake yi a fannin safarar albarkatun gonakin su, titin zai kuma share wata hanya ta inganta yawon shakatawa a yankin kudu maso gabashin Oromia, zai kuma samar da zarafin jawo karin masu yawon bude ido na gida da na waje zuwa yankin.
Masharhanta dai suna jinjinawa irin wadannan manyan ayyukan more rayuwa da kamfanonin Sin ke aiwatarwa a Habasha, musamman cikin shekarun baya bayan nan, inda bayanai suka nuna cewa, cikin shekaru 10 da suka shude, kamfanin gine-gine na CCCC kadai, ya aiwatar da muhimman ayyukan more rayuwa a Habasha, da suka hada da babbar hanyar ababen hawa mai tsawon kilomita 85, wadda ta hada birnin Addis Ababa zuwa Adama, da sabon zauren karbar baki na filin jirgin saman Bole dake Addis Ababa, da wasu yankunan masana’antu da dama, da suka hada da na Mekelle da Jimma.
Wadannan ayyuka na kara shaida cewa, hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, na ci gaba da zama muhimmin jigo, na cimma moriyar kasashen Afirka.