Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da gaggauta cire Birgediya Janar Muhammad Fadah a matsayin Darakta Janar na hukumar kula da ‘yan yi wa kasa hidima (NYSC) kasa da watanni shida da shigarsa ofis.
An nada Fadah, a matsayin Darakta-janar din NYSC a watan Mayun 2022 wanda ya karbi ragamar hukumar a hannun Manjo Janar Shuaibu Ibrahim.
- ‘Yansanda Sun Bai Wa NYSC Tabbacin Samar Musu Da Tsaro A Zamfara
- Ba A Samu Asarar Rai Ko Daya A Gobarar Da Ta Barke A Shalkwatar NYSC Ba – Hukuma
A wata sanarwar da Daraktan yada labarai na NYSC, Eddy Megwa, ya fitar a daren ranar Alhamis tare da aiko da kwafinta ga LEADERSHIP, bai dai bayyana cikakken dalilin da ya janyo wannan korar ba.
Sai dai wasu rahotonni sun yi nuni da cewa umarnin na Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na tsige shi bai rasa nasaba da rashin gogewarsa da kwarewarsa.
Kazalika, an ce wa Fadah ya mika ragamar shugabanci ga jami’in da ya fi kowani mutum girma a hukumar ta NYSC.
Jami’in da zai karbi ragamar a hannun Fadah zai tafiyar da hukumar na wucin gadi har zuwa lokacin da za a nada sabon Darakta Janar a hukumar.
A lokacin da Fadah ya karbi ragamar mulkin NYSC ya sha alwashin inganta tsaron mambobi masu yi wa kasa hidima da tababtar da Jin dadi da walwar ma’aikata da kyautata tsarin hukumar ta NYSC.