Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da Sarkin kasar Thailand Maha Vajiralongkorn Phra Vajiraklaochaoyuhua, da Sarauniya Suthida Bajrasudhabimalalakshana, jiya da dare a fadarsu.
Shugaba Xi tare da uwargidansa Peng Liyuan, sun dauki hotuna tare da tattaunawa da Sarki Vajiralongkorn da Sarauniya Suthida da kuma Gimbiya Sirivannavari Nariratana.
A cewar shugaba Xi, a bana ake cika shekaru 10 da kulla huldar abokantaka da hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni tsakanin kasashen biyu, kuma Sin za ta ci gaba da hada hannu da Thailand wajen daukaka dangantakar dake tsakaninsu ta iyali guda, wajen gina al’ummar Sin da Thailand mai makoma ta bai daya, da kuma kai dangantakarsu zuwa sabon matsayi.
A nasa bangare, Sarki Vajiralongkorn, ya ce karkashin kyakkyawan shugabancin Xi Jinping, kasar Sin ta kara karfi da samun ci gaba, yana mai matukar jinjinawa nasarori na ban mamaki da aka cimma karkashin shugaba Xi, musammam ma na kakkabe talauci da ingnata rayuwar jama’a.
Kana kuma, shugaba Xi Jinping, da Firaministan kasar Thailand Prayut Chan-o-cha, sun amince da gina al’umma mai makoma ta bai daya ta Sin da Thailand mai karfi da ci gaba da kuma dorewa.
Wannan na kunshe ne cikin sanarwar hadin gwiwa da aka fitar bayan ganawar shugabannin biyu a yau Asabar. (Fa’iza Mustapha)