Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da nadin Alhaji Yakubu Muhammad Kwairanga a matsayin sabon Sarkin masarautar Funakaye da ke jihar.
Nadin wanda ke kunshe ta cikin wasika da kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarakuna na jihar, Alhaji Ibrahim Dasuki Jalo, ya sanya hannu kamar yadda wata sanarwar da Kakakin gwamnan Ismaila Uba Misilli ya aiko wa LEADERSHIP Hausa a ranar Litinin ta nuna.
A cewar kwamishinan, gwamnan ya yi amfani da dokar kula da masarautu ta jihar Gombe na shekarar 2022 gami da kuma da amfani da shawararorin da masu alhakin zabin sabon Sarkin na masarautar Funalaye suka ba shi wajen nada Sarkin.
Kwamishinan, Hon. Dasuki, a lokacin da ke mika takardar ga sabon Sarkin a masarautarsa da ke Bajoga da ke karamar hukumar Funakaye, ya bukaci sabon Sarkin da ya yi kokarin rungumar kowa da kowa wajen bunkasa zaman lafiya da kwanciyar hankali kamar yadda magabatansa suka yi.
Ya ce, “Allah ta’ala ya zabi Yakubu Muhammad Kwairanga a matsayin sabon Sarkin wannan masarautar daga cikin mutane da dama da suka nema daga cikin wannan ahlin, ina rokon dukkanin al’ummar Funakaye da su mara wa sabon Sarkin baya.”
Ya bada tabbacin cewa gwamna Inuwa zai cigaba da mutunta sarakunan gargajiya lura da irin rawar da suke takawa wajen kyautaya zaman lafiya a cikin al’umma.
Da ya ke masa fatan yin mulki cikin nasara, kwamishinan ya ce bikin miki sandar mulki zai gudana daga baya.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa sabon Sarkin Kani ne ga marigayi Sarki Muazu Muhammad Kwairanga III da ya rasu a ranar 27 ga watan Augusta na 2022.