Ana fargabar cewa an kashe sojojin Nijeriya da dama yayin da wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar ta’adda ta ISWAP ne suka kai harin a wasu sansanonin sojoji guda biyu a jihar Borno.
Kamfanin dillancin labara na AFP ya bayar da rahoton cewa, harin da aka kai a ranakun Juma’a da Asabar a sansanin soji da kuma wani gari a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya, ya yi sanadin mutuwar sojoji tara da ‘yan sanda biyu da fararen hula, kamar yadda majiyoyin tsaro da mazauna yankin suka rahoto.
Rahoton ya ce wadanda ake zargin ‘yan kungiyar ISWAP ne a cikin manyan motoci dauke da bindigu masu jigida, sun kaddamar da hare-haren ne a Malam Fatori da ke gundumar Abadam da yammacin Juma’a da kuma safiyar Asabar.
“‘Yan ta’addar ISWAP sun kai wa Malam Fatori hari inda suka yi barna mai yawa wanda haka muke kokarin tantance adadin barnar,” inji wani jami’in soja da ya shaida wa AFP.
“Sun kai harin ne a sansanin sojoji inda sojojin suka yi artabu da su sannan kuma wani bangaren ‘yan ta’addan na biyu ya kai hari cikin garin,” in ji jami’in da ya nemi a sakaya sunansa.
Harin farko da aka kai a kusa da kan iyakar Jamhuriyar Nijar, ya zo ne da yammacin ranar Juma’a, wanda ya kai ga fafatawa da sojoji da suka dakile harin, in ji Buji Garwa mazaunin garin.
A wani harin da aka kai wa sansanin da cikin garin a ranar Asabar din da ta gabata, mayakan ISWAP sun jefa bama-bamai tare da kashe mazauna garin, yayin da wasu kuma suka nutse a cikin kogin da suke kokarin tserewa daga harin.