Ministan sufurin jiragen kasa Mu’azu Jaji Sambo ya sanar da cewa, kamar yadda aka tsara za a dawo da zirga-zirgar jirgen kasa daga Abuja zuwa Kaduna a yau litinin, hakan ba zai yiwu ba.
Mu’azu ya sanar da hakan ne a lokacin da yaje duba aikin dawo da zirga-zirgar jirgin kasan daga Abuja zuwa Kaduna a jiya lahadi, inda ya ce, an kara wa’adin dawo da zirga-zirgar jirgin kasan daga Abuja zuwa Kaduna zuwa nan da mako daya domin samun damar fadakar da fasinjojin kan sabbin tsare-tsaren hawa jirgin da kuma sauran abubuwan da ake bukata su yi.
Ya ci gaba da cewa, an samar da tsaro a kan hanyar kuma an shirya tsaf don jirgin ya fara gudanar da aiki akan hanyar, amma akwai sabbin abubuwan da ake bukata, musamman wajen sayen tikitin hawa jirgin, a saboda hakan, akwai bukatar a dage dawo da aikin zuwa mako daya.
Mu’azu ya kara da cewa, maganar cewa ko jargin za a iya dawo da ci gaba da aiki ayau ko kuma ba haka ba, bamu sanar cewa jirgin zai dawo aiki a ayau litinin ba, inda ya ce, a yanzu mun fito da wani sabon tsari na kafin a sayarwa da fasinja tikiti wanda sai fasinja ya bayar da lambar wayarsa, katinsa na shedar dan kasa, wanda wannan shine, matakin tsaro na farko.
Ministan ya ce, hakan zai taimaka mana wajen sanin lokacin da jirgin ya tashi daga wata tasha zuwa wata tasha da kuma sanin adadin fasinjojin da ke cikin jirgin, inda ya kara da cewa, idan fasinja bai da katin dan kasa, ba za a barshi ya shiga jirgin ba.
Ya ce, idan yaro ne, manyan za su biya masa da kuma yi masa rijista, inda su kansu manyan, an kayyade ba za su yiwa yara sama da hudu ba.
A cewarsa, a yanzu muna son mu bayar da isasshen lokaci domin ‘yan Nijeriya su san wannan sabon tsarin da muka fito dashi.