‘Yansanda a jihar Ogun sun kama wata budurwa ‘yar shekara 29 mai suna Chioma Okafor da kuma wani matashi mai suna Nweke Joshua, bisa zarginsu da yunkurin yin amfani da bindigar roba don yin fashi a anguwar Adesan da ke yankin Mowe.
A cikin sanarwar da kakakin rundunar ‘yansandan jihar Abimbola Oyeyemi ya baiwa manema labarai a garin Abeokuta ya ce, an cafke su ne biyo bayan kiran wayar gaggawa da aka yiwa ofishin ‘yansandan Mowe.
Ya ce, an sanar da jami’an cewa, ‘yan fashi sun je yin fashi a wani shagon sayar da kayan masarufi mallakar wani mai suna Johnson Nwokoro da ke a mahadar ababen hawa ta Safari, inda kuma suka yiwa mai shagon fashi.
Oyeyemi ya ce, bayan samun kiran wayar, DPO na ofishin ‘yansandan na Mowe SP Folake Afeniforo ya yi gaggawar tura Jami’ansa zuwa yankin, inda suka cafko wadanda ake zargin.
Ya ce, bayan jami’an sun cafke su, sun gano cewa, sun zo shagon ne domin yin fashin da bindigar roba, wacce ta yi kama da ta gaske.
Oyeyemi ya ce, kwamishinan rundunar Lanre Bankole, ya bayar da umarnin a tura su zuwa sashen bincike na SCI domin a ci gaba da gudanar da bincike.