Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), ta umarci wasu zababbun ofisoshin da ke yin fasfo a sassan kasar nan da su tsawaita ayyukan da suke gudanarwa na fasfo har zuwa ranakun karshen mako, don biyan bukatun tulin jama’a masu neman takardun fasfo da ke jibge a kasa.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin sanarwar da jami’in watsa labarai na hukumar, Mista Tony Akuneme, ya fitar a Abuja.
- 2023: Ba Ni Da Kudurin Mayar Legas Birnin Tarayyar Nijeriya – Tinubu
- Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Hutun Mako 2 Ga Ma’aikata Maza Da Matansu Suka Haihu
A cewar Akuneme, Kwanturola-Janar na NIS, Idris Isa Jere, ne ya bayar da wannan umarnin, kuma ya amince da gaggauta kai kwanturolan sashen fasfo zuwa Jihohin Ekiti da Jigawa, sannan kuma wanda ke Ondo za a mayar da shi zuwa ofishin shiyya na hukumar da ke Ibadan.
A cewarsa, wannan sabon umarnin na daga cikin kokarin da ake son cimma wajen rage tulin bukatun fasfo da suka taru a tsakanin 2020 zuwa 2021 sakamakon kullen annobar Korona.
“Kwanturola-Janar, ya umarci ofisoshin a sassan kasar nan da ke da tulin bukatun fasfo da yawa a hannunsu da suke gudanar da ayyukansu har da ranukan Asabar.
“Ana sa ran wannan aikin zai ke guduna duk ranar Asabar da zai fara aiki daga ranar 3 ga watan Disamban 2022 har zuwa ranar 28 ga watan Janairun 2023 daga karfe 10 na safe zuwa karfe 2 na rana,” a cewar sanarwar.
Kazalika, Kwanturola-Janar din, ya gargadi jami’an da ke kula da aikin samar da fasfo da su maida hankali wajen gudanar da ayyukansu yadda ya dace, ya gargadin dandana wa dukkanin jami’in da aka kama da saba ka’idar aiki.
Ana sa ran wannan mataki zai taimaka sosai wajen saukaka wa jama’a masu neman fasfo musamman a lokutan bukukuwan sabuwar shekara da na Kirsimeti.