Wani Lauya mai rajin kare hakkin bil’adama, Monday Ubani ya caccaki uwargidan shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari kan yadda tasa aka kama Aminu Adamu bisa zargin yi mata izgili a shafin sada zumunta.
A cewarsa, ‘yan Najeriya da dama sun yi wa Misis Patience Jonathan cin fuska da dama a lokacin da mijinta ke shugabantar Nijeriya daga 2010 zuwa 2015 amma ba ta kama wani daga cikin masu batancinta ba.
Ubani, wanda shi ne shugaban kungiyar lauyoyi ta Nijeriya mai kula da ‘yan cin ra’ayin jama’a da dokar ci gaban jama’a (SPIDEL) ya kalubalance Uwargida Aisha Buhari ne yayin da ya bayyana a wani shiri mai suna ‘Sunrise Daily’ na gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis.
Ya bukaci masu rike da mukaman gwamnati da matansu da su kasance masu hakuri domin a kullum mutane za su rika sukarsu da ayyukansu.
“Matar tsohon shugaban kasa, Misis Jonathan, so da dama, an ta yada ta a shafukan sada zumunta don izgili a gareta, ana kiranta da sunaye daban-daban amma ba mu taba jin inda ta umarci jami’an tsaro da su kama ko daya daga ciki b.