Masu garkuwa da mutane sun saki Basaraken gargajiya ‘Oloso’ na Oso Ajowa a karamar hukumar Akoko ta Arewa Maso Yamma a jihar Ondo, Oba Clement Omoola Jimoh, bayan shafe tsawon mako guda a hannunsu.Â
Majiyoyi daga iyakansa sun cewa Oba Jimoh ya kubuta ne a ranar Laraba kuma yanzu haka yana karkashin kulawar Likitoci domin duba halin lafiyarsa a wani asibitin da ba a bayyana sunansa ba.
Masu garkuwan dai sun kutsa kai cikin gidan Sarkin a ranar Alhamis din da ta gabata inda suka saceshi da karfin tsiya tare da yin harbe-harbe, kuma garkuwa da shi din ya janyo tashin hankali a yankin Oso-Ajowa da Akokoland da ke jihar.
Sai dai ba a tabbatar wa duniya cewa an biya kudin fansa ko ba a biya ba kafin sake Sarkin ba.
Su dai masu garkuwan sun bukaci kudin fansa na miliyan 100 amma daga baya suka rage zuwa miliyan 10.
Lokacin da jama’an Ajpwa Okoko suka samu labarin sakin na Basaraken sun Yi ta murna bisa samun nasarar fitowar basarakensu.