Shawarar “ziri daya da hanya daya”, shawara ce da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a shekarar 2013. Da farko shawarar ta mayar da hankali ne kan zuba jari a fannin ababen more rayuwa, da ilimi, da gine-gine, da hanyoyin mota da layin dogo, da rukunin gidajen kwana, da tashoshin samar da wutar lantarki, da sauran muhimman fannoni da dan-Adam ke bukata.
Bayanai na nuna cewa, shawarar ta kasance tsarin da ya gudanar da ayyukan more rayuwa da zuba jari mafi girma a tarihi, inda ya shafi sama da kasashe 68, ciki har da kaso 65 cikin 100 na yawan al’ummar duniya, da kaso 40 cikin 100 na ci gaban GDPn duniya a shekarar 2017.
Shawarar “ziri daya da hanya daya” ta magance gibin ababen more rayuwa, kana tana da karfin bunkasar tattalin arziki a yankin Asiya da Fasifik da yankunan tsakiya da gabashin Turai. Masana sun yi imanin cewa, shawarar tana da muhimmanci wajen bunkasa alakar kasa da kasa. Kuma yanzu haka, akwai kasashe kimanin 140 da kungiyoyin kasa da kasa sama da 28 da suka sanya hannu kan shawarar. Duk da yadda wasu kasashen yamma ke yi mata bahaguwar fahimta.
Saboda muhimmanci da tasirin da shawara ke kara yi a sassan duniya, yanzu haka an sanya shawarar cikin muhimman takardun manyan hukumomin kasa da kasa misali, MDD, da kungiyar G20, da kungiyar raya tattalin arzikin Asiya da Fasifik da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da sauransu.
Duk da sauye-sauye da yanayi na rashin tabbas da ra’ayin ba da kariya ga harkokin cinikayya da ra’ayi na kashin kai da duniya ke fuskanta a halin yanzu, shawarar da kasar Sin ta gabatar, wata dama ce da sauran kasashe za su amfana da irin ci gaba da ma fasahohin da kasar Sin ta samu.
Shawara ce da ke mutunta ra’ayoyi da ka’idojin kasashe da tuntubar juna da alaka ta samun nasara tare gami da nuna daidaito.
Bugu da kari, shawarar wani shiri ne da kasar Sin ta gabatar bisa buri guda da al’ummomin kasa da kasa ke da shi na samar da wadata ga duniya baki daya.
Taron kolin shawarar na biyu da ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin, ya kara tattauna matakan raya shawarar, ta yadda za ta amfani duniya baki daya. Tashar jiragen ruwa ta Lekki dake Ikko na tarayyar Nijeriya na iya zama misali wadda ta kasance wani muhimmin shirin hadin gwiwa da ake aiwatarwa tsakanin kasashen Sin da Nijeriya da ma Sin da nahiyar Afirka bisa shawarar “ziri daya da hanya daya”, wadda kamfanin CHEC na kasar Sin ya sa hannun zuba jarin aiki da gudanar da shi. Ana kuma fatan tashar za ta kasance daya daga cikin tashoshin jiragen ruwa masu zurfi kuma mafi girma a yammacin Afirka, bayan an gama aikin gina ta. Shawarar “ziri daya da hanya daya”, ta kasance hajar da kowa zai iya amfana da ita a duniya, wadda ta samu karbuwa tsakanin kasa da kasa, kana ta zama dandalin hadin gwiwa mafi girma a fadin duniya.
Duk da yadda annobar COVID-19 ke yaduwa a sassan duniya, hanyar siliki ta kiwon lafiya tana taka muhimmiyar rawa wajen rage radadin annobar da fita daga annobar da farfado da tattalin arziki. “Bisa shawarar, karkashin tsarin hanyar siliki ta kiwon lafiya, kasar Sin tana taimakawa kasa da kasa, ta kuma hada kai da kasashen duniya wajen nazarin alluran rigakafi, da samar da marufin baki da hanci, ba da agajin lafiya da sauransu, duk a kokarin rage radadin annobar ta fuskar kiwon lafiya da tattalin arziki, lamarin da ya nuna tunanin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil- Adam.
Don haka, shawarar na da muhimmanci matuka, wadda ake aiwatar da ita bisa ka’idar taimakawa juna, wadda ta kasance hanya mafi dacewa a duniya bayan barkewar annoba. Alkaluman da hukumar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, cikin watanni 8 na farkon bana, kasar ta samu nasarori a fannin zuba jari da hadin gwiwa da kasashen dake kan hanyar “ziri daya da hanya daya”, haka kuma zuba jari a bangarori daban-daban daga kasashen waje na karuwa. Yadda sakatariyar MDD ta raba shawarar “ziri daya da hanya daya” a matsayin wani kundi a babban zauren majalisar karo na 75, ya kara nuna kudirin al’ummar duniya na amincewa da hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya”.
A shekarar 2021 kamfanin talabijin na StarTimes na kasar Sin, ya shirya wata gasar gajerun hotunan bidiyo da nufin nuna ayyukan da aka gudanar a karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya” wato BRI a nahiyar Afrika.
A cewar StarTimes, gasar da aka shirya a karo na uku, ta karbi amsoshi daga ’yan Afrika, wadanda suka nuna yadda ayyukan da kasar Sin ta samar da kudin aiwatar da su a yankunansu, suka sauya rayuwar al’ummomin irin wadannan kasashe. Taken gasar shi ne “yayata damammaki domin samun kyakkyawar makoma” wanda ya mayar da hankali kan muhimman ayyukan more rayuwa, ciki har da layin dogo na zamani tsakanin biranen Mombasa da Nairobi a Kenya, da layin dogo tsakanin biranen Lagos da Ibadan a Nijeriya, da kuma na’urorin kama shirye-shiryen talabijin da rediyo na zamani na Mozambique.
Yayin babban taron hadin gwiwar kasa da kasa na yankin Asiya da Fasifik kan shawarar “ziri daya da hanya daya”, da aka gudanar ta kafar bidiyo. An bayyana cewa, an cimma matsaya game da batutuwa shida yayin taron, inda daukacin mahalartansa suka bayyana burin su, na kara gina dangantaka ta kut da kut tsakaninsu, an kuma kaddamar da shawara mai nasaba da hadin gwiwar samar da aluran rigakafi, da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba.
Wasu kwararru game da al’amuran kasa da kasa na yankin gabashin Afirka, sun bayyana shawarar “ziri daya da hanya daya” da kasar Sin ta gabatar, a matsayin manufar dake ingiza ci gaban nahiyar Afirka. Sun kuma bayyana cewa, shawarar ta zamo ginshikin aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa, da rage matsalar karancin guraben ayyukan yi, da bunkasa cinikayya da sauransu. Kuma sabanin yadda kasashen yamma ke zargi, idan aka dubi ci gaban da nahiyar Afirka ke samu a fannin samar da ababen more rayuwa, za a fahimci irin taimako da shawarar take baiwa nahiyar. Hakika kasar Sin na samar da agaji irin wanda kasashen Afirka ke bukata.
Bugu da kari, shawarar “ziri daya da hanya daya”, ta baiwa kasar Sin damar raba dabarun ci gabanta da sauran kasashen Afirka masu tasowa, wanda hakan ya haifar da nasarar kammala layin dogo da ya hade biranen Mombasa da Nairobi, aikin dake taka muhimmiyar rawa a fannin bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar Kenya. Bayanai na nuna cewa, tun bayan da aka gabatar da shawarar, ya zuwa yanzu kasar Sin ta yi aiki tare da kasashen da abin ya shafa, wajen zurfafa hadin gwiwar moriyar juna bisa ka’idar yin shawarwari mai zurfi, da ba da gudummawar hadin gwiwa, da samun moriyar juna, kana ta cimma nasarori masu tarin yawa.
Kuma yanzu haka, akwai kasashe kimanin 140 da kungiyoyin kasa da kasa sama da 28 da suka sanya hannu kan shawarar, duk da yadda wasu kasashen yamma ke yi mata bahaguwar fahimta. Yayin dandalin tattaunawar hadin gwiwar kafofin watsa labarai na kasashen dake cikin shawarar “ziri daya da hanya daya” na shekarar 2022 da ya gudana a birnin Xi’an dake jihar Shaanxi ta kasar Sin, shugaban hukumar yada manufofin kwamitin kolin JKS na wancan lokaci Mr. Huang Kunming ya bayyana cewa, raya shawarar “ziri daya da hanya daya” cikin hadin gwiwa, wani babban shiri ne da Shugaba Xi Jinping ya gabatar, bisa tsarin bunkasuwar duniya da bukatun ci gaban da aka cimma a wannan zamani, da inganta gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil-Adama. Kafofin watsa labarai suna taka muhimmiyar rawa matuka wajen yada bayani, da inganta yarda da juna da kulla yarjejeniya da sauransu. Raya shawarar “ziri daya da hanya daya” ba zai samu ba, sai da hadin kai da himma na kafofin watsa labarai na kasashe daban daban, da kuma sadarwa na zahiri da hadin gwiwa da juna.
A nan gaba, ya yi fatan galibin abokan kafofin watsa labarai, za su gada da kuma yada ruhin hanyar siliki, da himmatuwa wajen yada ra’ayin wayewar kai na daidaito, da koyi da juna, da tattaunawa da hadin kai, da magana da kalamai masu dacewa, don neman ci gaba cikin hadin gwiwa, da kara kaimi don samun nasara, da kuma yadda kafofin watsa labarai za su bayar da gudummawa don gina shawarar “ziri daya da hanya daya” mai inganci tare.
Bayanai sun nuna cewa, kasar Sin tana kokarin gina layukan dogo a kasashen nahiyar Asiya, da Turai, da arewacin Amurka, da kuma Afirka, wadanda suka zama shaidun aikin raya shawarar “ziri daya da hanya daya” da kuma hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a wannan fanni. Kamar yadda tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana, layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi, ya samar da kyakkyawar makoma ga dukkan jama’ar kasar a fannonin samun ayyukan yi da wadata. Wannan yana kara shaida cewa, ya kamata a yi hadin gwiwa da samun moriyar juna da adalci da wadata tare, wanda zai taimaka ga ci gaban sassan duniya baki daya. Ya ce, Sin za ta ci gaba da kokari tare da bangarori daban daban, don sa kaimi ga raya shawarar “ziri daya da hanya daya” da bayar da gudummawa ga samun ci gaba da wadata na bai daya a duniya.
Game da sabuwar shawarar inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, wadda kasashen G7 suka gabatar kuwa, har kullum kasar Sin tana maraba da duk wata shawarar dake inganta muhimman ababen more rayuwar al’ummar duniya, kana shawarwari daban-daban ba za su iya maye gurbin juna ba. Sai dai kuma, tana nuna adawa da duk wani yunkuri na bata sunan shawarar “ziri daya da hanya daya”, bisa hujjar inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, don cimma muradun siyasa. Sabbin alkaluman da babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Yuli na wannan shekarar, jimillar kudin da aka samu daga kayayyakin da aka shigo da su da wadanda aka fitar a tsakanin kasar Sin da kasashen dake bin shawarar “ziri daya da hanya daya”, sun kai Yuan tiriliyan 6.3, adadin da ya karu da kashi 25.5 cikin 100. Kuma daga cikin su, adadin da kasar ta fitar na kaya ya karu, da kashi 25.3 bisa 100, yayin da aka shigo da kayayyakin da darajar adadin su ya karu da kashi 25.7 cikin 100.
A matsayinsa na babban aikin hadin gwiwa game da shawarar “ziri daya da hanya daya”, layin dogo tsakanin Lagos zuwa Ibadan, wanda ya kasance layin dogo na zamani na farko a yammacin Afirka da kamfanin kasar Sin ya gina, ya soma aiki a kwanan nan. Wannan layin dogo ya hada Lagos, birni mafi girma a Afirka, kuma cibiyar tattalin arzikin Najeriya, da Ibadan, babban birnin masana’antu a kudancin kasar, ya kuma kyautata yanayin sufuri a kudancin Najeriya, da bude babbar hanyar ci gaban tattalin arzikin cikin gidan kasar. Shi ma, layin dogo tsakanin Sin da Laos mai taswon kilomita 1,035 da aka gina karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, ya samar da hanya mai inganci da saukin zirga zirga tsakanin kasashen 2, da taimakawa wajen gudanar da hidimomin aikewa da hajoji tsakanin Sin da mambobin kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya. Ya zuwa yanzu, kimanin fasinjoji sama da miliyan 8.5 ne suka yi zirga-zirga, kan layin dogo yayin da adadin hajoji da aka yi dakon su ta layin dogon, ya kai tan miliyan 11.2, tun bayan bude shi shekara guda da ta gabata. Haka kuma layin dogon ya hade birnin Kunming na lardin Yunnan na kasar Sin da Vientiane fadar mulkin kasar ta Laos. Yawan kasashen da suka kulla yarjejeniyar hadin gwiwa bisa shawarar tare da kasar Sin, sun kai 140. Har ila yau, jimillar cinikayya da aka yi tsakanin Sin da abokan cinikayyarta bisa shawarar ya zarce dalar Amurka tiriliyan 9.2, kana jimillar jarin da kamfanonin Sin suka zuba kai tsaye a kasashen da abin ya shafa, ya wuce dalar Amurka biliyan 130. Ko shakka babu shawarar “ziri daya da hanya daya”, ta zama wani babban dandalin hadin gwiwa na kasa da kasa mafi girma a duniya.
(Ibrahim Yaya)