A karon farko a matsayinsa na Shugaban kasar Amurka, Joe Biden zai kai wata ziyara yankin Gabas ta Tsakiya.
BBC ta wallafa a shafinta cewa, ana sa ran shugaban zai kai ziyara Æ™asashen Saudiyya da Isra’ila da kuma wasu yankunan Palestine.
Shugaban zai yi tafiyar ne a watan Yuli mai zuwa inda zai shafe kwana huÉ—u yana rangadi.
Mista Biden dai zai kafa tarihi a matsayinsa na Shugaban Amurka idan ya je Saudiyya daga Isra’ila – hanya ce ta jirgi da Saudiyya ba ta cika bari ana bi ba sakamakon rashin jituwa irin ta diflomasiyya tsakanin Isra’ila da Saudiyya.