A ranar Asabar 10 ga watan nan, jakadan Amurka dake kasar Sin Burns R Nicholas, ya fitar da wata sanarwa, albarkacin ranar kare hakkin bil adama ta duniya, inda ya yi tsokaci game da abun da ya kira yanayin da hakkin bil adama ke ciki a kasar Sin.
Game da hakan, yayin taron manema labarai na Litinin din nan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce jerin sanarwar da bangaren Amurka ya rika fitarwa, na kunshe da zargin kasar Sin a fannin kare hakkin bil adama, zargin da kuma ba shi da tushe ko makama.
Wang Wenbin, ya ce zantukan bangaren Amurka cike suke da karairayi da kiyayya, da alamu na halayyar Amurka ta yin babakere, sun kuma fallasa aniyar kasar ta siyasar tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, da yin karan-tsaye ga ci gaba, da moriya, da hadin kan sassan kasar Sin, duk ta hanyar fakewa da kare hakkin bil adama. Don haka dai kasar Sin na matukar bayyana bacin rai, da kuma adawa da hakan. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa)