Yayin da zabukan shekarar 2023 ke kara kara gabatowa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi gargadi da kakkausar murya ga ‘yan Nijeriya.
Hukumar INEC ta ce tana sane da cewa wasu ‘yan siyasa sun tsunduma cikin sayen katin zabe na dindindin (PVCs) daga ‘yan Nijeriya masu fama da yau da gobe.
INEC ta yi gargadin cewa duk wanda aka kama yana sayar da PVC dinsa wanda hakan ya saba wa dokar zabe, don haka, za a kai shi kotu ya fuskanci hukunci.
Hukumar wacce ta yi wannan gargadin a ranar Litinin din da ta gabata, ta kuma zargi batagarin ‘yan siyasa da kokarin siyan lambobin katin zaben ga marasa galihu don yin kokarin tafka magudi a zaben dake karatowa, amma ba za suyi nasara ba.