Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta amince da cewa ‘yan Nijeriya da ke son komowa gida bayan fasfo dinsu na Nijeriya ya kare, za su iya dawowa gida.
Wannan na kunshe ne a cikin wata wasika daga Babban Kwanturolan Hukumar Kula da Shige da Fice (CGIS) Isah Jere Idris, zuwa ga Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama mai kwanan wata 9 ga Disamba 2022.
“Saboda haka, an bukaci dukkan kamfanonin jiragen sama da su kyale masu rike da fasfo din Nijeriya da ya kare su shiga ba tare da wata tsangwama ba.
“Bugu da kari, ana kira ga dukkan jami’an diflomasiyyar Nijeriya da ke kasashen waje da su mika wadannan bayanai ga kamfanonin jiragen sama da hukumomin kan iyaka na kasashen da ke karbar bakuncin ‘yan Nijeriya,” in ji wani bangaren wasikar.