A yau ne, sashen kula da matakan yaki da cutar COVID-19 na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya gudanar da taron manema labaru, inda aka yi bayani game da yanayin da jama’a ke karbar alluran rigakafin cutar COVID-19 a kasar Sin.
Ya zuwa ranar 13 ga watan Disamba na shekarar 2022, yawan alluran rigakafin cutar COVID-19 da aka karba a kasar Sin, ya kai miliyan 3451 da dubu 677, kimanin kashi 92.73 cikin dari na adadin mutanen kasar Sin suka karbi allurar.
Yawan tsofaffi masu sama da shekaru 60 da haihuwa a Sin da suka karbi alluran rigakafin cutar COVID-19, ya kai miliyan 240 da dubu 219, adadin da ya kai kashi 91 cikin dari na adadin tsofaffin kasar. (Zainab)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp