Wata gobarar da ta tashi ta kone duron man fetur da dizal 350 a yammacin ranar Laraba, a cewar hukumar kashe gobara ta Adamawa. Lamarin ya afku ne a wurin ajiyar man da ke Yola babban birnin jihar.
Daraktan hukumar kashe gobara na jihar Adamawa, Adamu Abdullahi, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a yammacin ranar Alhamis, inda ya kara da cewa wata babbar mota da ke dakon man itama ta kone kurmus.
Man fetur da Dizel din da suka kone, mallakar wani mai suna Ibrahim ne da akafi sani da Mai Injin Oil, acewar hukumar kashe gobarar, ana sarrafa wajen man fetur din ne ba bisa ka’ida ba.
Adamu ya kara da cewa, gobarar da ta tsallaka makobta baccin hukumar kashe gobara ta kawo dauki cikin gaggawa.
Ya ce, hukumar za ta kara kai ziyara wurin domin sanin yawan barnar da gobarar ta yi.