Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Geng Shuang ya bayyana a jiya cewa, Sin ta yi kira ga bangarori daban-daban na kasar Libya da su warware matsalolinsu a siyasance, da yin hakuri da juna bisa karfinsu da kiyaye zaman lafiya da aka wanzar da shi cikin wuya.
Geng Shuang ya bayyana haka a taron tattauna kan batun Libya na kwamitin sulhu na MDD, an jinkirta zaben Libya har tsawo shekara guda tun daga ran 24 ga watan Disamba na bara.
A cikin wadannan lokuta, bangarori daban-daban da abin ya shafa a Libya ba su kai ga matsaya daya kan halastaciyyar gwamnati ba, har an tada rikice-rikice, amma wasu ayyukan dake taka rawa ga bunkasuwa da dunkulewar kasa ba su samun ci gaba ba ko kadan.
Sin na fatan bangarorin sun maido da sulhuntawa tun da wuri karkashin shiga tsakanin wakilin musamman na babban magatakardan MDD. Abin da aka sa gaba shi ne kai ga matsaya daya kan tushen tsarin dokar zabe ba tare da bata lokaci ba, ta yadda za a gudanar da zabe tun da wuri don kawo karshen barakar kasar da samarwa kasar wani yanayin siyasa mai kyau wajen farfado da kasar.
Geng Shuang ya ce, MDD hanya mafi muhimmanci wajen shiga tsakanin batun Libya. Sin ta yi kira ga zamantakewar al’ummar duniya da su tabbatar da ka’idar bar Libya ta daidaita harkokinta bisa karfin kanta da ba da taimako yadda ya kamata, da mutunta cikakken tsarin mulki da dunkulewar kasar Libya. Ban da wannan kuma, nuna goyon baya ga MDD da ta shiga tsakanin batu, kada a tsoma baki ko nuna karfin tuwo kan lamarin. (Amina Xu)