Ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, ta ce matakan da Amurka ke aiwatarwa na kashin kai, da baiwa kasuwa kariya, na yin mummunar illa ga harkokin samar da hajoji daga masana’antun kasa da kasa. Kaza lika hakan ya sabawa ka’idojin raya tattalin arziki da hada hadar kasuwanni.
Tsokacin na ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, ya biyo bayan wata tambaya ce da aka gabatar, game da zama na 15 na kungiyar cinikayya ta duniya WTO, game da nazarin manufofin cinikayyar kasar Amurka, wanda ya gudana a farkon makon nan.
Yayin zaman dai, kasar Sin ta bayyana damuwa game da matakan da Amurka ke aiwatarwa, kamar samar da gatanci mai yawan gaske ga bangare guda, da daukar matakan kashin kai masu nasaba da kakaba harajin cinikayya, bisa fakewa da kuduri mai lamba 301, tare da daukar matakan da ba su dace ba wajen kayyade fitar da kayayyaki zuwa ketare.
Sauran mambobin WTO, ciki har da kungiyar tarayyar Turai ta EU, da kasashen Japan da Canada, su ma sun bayyana damuwa yayin zaman, duba da yadda matakan Amurka na gudanar da cinikayya, da daukar matakan kashin kai a fannin, ke yin mummunan tasiri ga harkokin kasuwancin duniya.
Nazarin manufofin cinikayya, na daya daga cikin ayyuka 3 da WTO ke gudanarwa, kuma zaman muhimmin dandali ne dake baiwa mambobin WTO damar morar ikon su, da kuma bayyana mahangarsu game da batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya. (Saminu Alhassan)