Jiya Asabar 17 ga wata ne, aka rufe babban taro a mataki na biyu, na sassan da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kare mabambantan halittu ta Majalisar Dinkin Duniya karo na 15, ko COP 15 a takaice a kasar Kanada, inda shugaban taron, wanda kuma shi ne ministan kula da muhallin halittun kasar Sin, Huang Runqiu, ya jagoranci bikin rufe taron.
Bangarori mahalarta taron sun bayyana fatansu, na aiwatar da “tsarin kasancewar mabambantan halittu a duniya bayan shekara ta 2020” ba tare da bata lokaci ba.
Huang ya ce, an cimma tudun-dafawa, a yayin babban taron na yini biyu na COP 15. A lokacin bikin bude taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabin dake kunshe da “wasu shawarwari hudu”, dangane da kiyaye halittu daban-daban a duniya, al’amarin da ya sanya babban kuzarin siyasa, ga ayyukan kare mabambantan halittun duniya.
Ita ma a nata bangaren, sakatariyar zartaswa daga sakateriyar yarjejeniyar kare mabambantan halittu ta MDD, Elizabeth Maruma Mrema, ta ce jawabin shugaba Xi yana cike da bayanai masu muhimmanci, inda ya jaddada muhimmancin kasancewar bangarori daban-daban a harkokin duniya, da yin kira da a zurfafa hadin-gwiwa da mu’amala tsakanin kasa da kasa, don neman cimma maslaha, da shirya “tsarin kasancewar mabambantan halittu a duniya bayan shekara ta 2020”.
Shugaba Xi ya kuma ambaci alfanun dake tattare da kyautata tsarin muhallin halittu, al’amuran da suke da matukar muhimmanci ga samar da ci gaba a fannin gudanar da shawarwari. (Murtala Zhang)