Asusun raya kasar Sin da kasashen Afirka, asusun da bankin raya kasar Sin ke gudanarwa, ya sanar da cewa, ya zuwa yanzu ya zuba jarin sama da dalar Amurka biliyan 5 a kasashen Afirka.
Bangarorin da asusun ya zuba jarin sun hada da ababen more rayuwa, da aikin noma, da rayuwar jama’a, da inganta hadin kai a masana’antu, da wuraren raya masana’antu, da sauran fannoni, kuma jarin ya taimaka wajen habaka tattalin arzikin kasashen Afirka, da samar da ayyukan yi, da kudaden shiga na haraji a Afirka.
Asusun ya dimbin jarin a fannoni da dama a Afirka, lamarin da ya zama abun misali wajen kara azama kan aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya” cikin hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka.
An kafa asusun ne a shekarar 2007, bayan kammala taron kolin na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka (FOCAC) na shekarar 2006 a birnin Beijing domin tallafa wa kamfanonin kasar Sin dake nahiyar Afirka, inda ya fara da jarin dalar Amurka biliyan 5 a karon farko.
Ya zuwa yanzu, asusun ya yanke shawarar zuba jarin sama da dalar Amurka biliyan 6.6 a wasu ayyuka a kasashen Afirka 39, ya kuma jawo jarin sama da dalar Amurka biliyan 31 daga kamfanonin kasar Sin.(Ibrahim)