Kididdigar baya bayan nan ta nuna cewa, a jiya Talata, jigilar kayayyaki na kasa tana gudana cikin tsari, kuma bangaren sufurin jiragen sama ya ba da tabbacin jigilar kayayyaki ta karu da kashi 37.6% bisa watan da ya gabata.
Bisa kididdigar da ofishin kula da ayyukan tabbatar da jigilar kayayyaki na majalisar gudanarwar kasar ya fitar, a jiya Talata, sufurin jiragen kasa na kasar, ya ci gaba da aiki bisa babban mataki, inda ya yi jigilar kayayyaki tan miliyan 10.833, wanda ya karu da kashi 0.09% bisa watan da ya gabata. Yawan motocin da suka yi zirga-zirga a kan manyan hanyoyin kasar ya kai miliyan 6.7704,wanda ya karu da kashi 1.85% bisa watan da ya gabata. Bangaren sufurin jiragen sama ya ba da tabbacin jigilar kayayyaki har sau 618, daga cikinsu, akwai jiragen saman jigilar kayayyaki na kasa da kasa sau 432 da na cikin gida 186, adadin da ya karu da kashi 37.6% bisa watan da ya gabata. Haka kuma, Yawan kayayyakin sakonni da gidan waya ya karba ya kai kusan miliyan 260, wanda ya ragu da kashi 2.6% bisa watan da ya gabata. (Safiyah Ma)