Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana cewa, kasar Sin za ta kara saukaka mu’amalar jami’an da ke kan iyaka, bisa la’akari da yanayin da ake ciki.Â
Mao Ning ta bayyana hakan ne, yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa Larabar nan, lokacin da take amsa wata tambaya game da ko kasar Sin, na da wani shiri na inganta matakan killace masu shigowa cikin kasar.
Mao ta ce, tun bayan bullar cutar COVID-19, kasar Sin ta dauki managarcin tsarin yaki da annobar, tare da samun nasara a wannan fanni. Tana mai cewa, kasar Sin ta kasance a kan gaba wajen dawo da aiki da samar da kayayyaki a duniya baki daya, baya ga sa kaimi ga kara bude kofa ga jama’a, da inganta manufofin samun takardar iznin shiga kasar wato Visa ta hanyoyin masu sauri.
Haka kuma kasar Sin ta kara yawan zirga-zirgar jiragen sama na kasa da kasa bisa tsari, da saukaka matakan dakilewa da hana yaduwar cutar, da saukaka musaya tsakanin jama’a, kuma hakan suna ba da muhimmiyar gudummawa ga zaman lafiyar masana’antu da tsarin samar da kayayyaki a duniya. (Mai fassara: Ibrahim Yaya)