Wata wutar lantarki mai karfi a wasu yankunan Zariya cikin Gwargwaje da Kauran Juli da ke kan hanyar Zariya zuwa Kaduna, ta kashe mutane 11.
Wani mazaunin yankin, Malam Abdullahi Tanimu, ya ce, “An dawo da wutar lantarkin ne da karfin gaske a yankin da misalin karfe 1:0 na dare, hakan ya haifar da tartsatsin wuta daga wayoyin na’urorin lantarkin ta wurare mabanbanta.” Inji rahoton newspotng.com
Ya ce wutar lantarkin ta kona gidan wani Injiniya Zubair Abubakar, sauran gidajen jama’a kuma sai hayaki ne ke ta fita.
Ya ce daga cikin wadanda wutar lantarkin ta kashe sun hada da; mace mai ciki, ma’aikatan lafiya, da dan sanda, da sauran mutane.
Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, shugaban sashen sadarwa na kamfanin samar da wutar lantarki na Kaduna (KEDCO), Abdulazeez Abdullahi, ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon sabanin tashoshin lantarki, babban layin wuta ya sauka a kan karamin layi wanda hakan ya haifar da tartsatsin wutar.