An kammala shirin kare kasafin na makonni biyu da ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnati suka gudanar a gaban kwamitin kula da kare kasafin kudin na majalisar dokokin Jihar Katsina.
Shirin wanda shugaban kwamitin Alhaji Sabiu Muduru ya jagoranta ya tattauna a kan kiyasin kasafin kudi na sashen shirin dorewar muradin karni, da na hukumar kyautata jin dadin alhazai ta jaha da na hukumar kula da ilimin Islama da kuma na hukumar shari’a.
- Bayan Hukuncin Kotu, Dan Takarar Sanata Na APC A Nasarawa Ya Bai Wa Magoya Bayansa Hakuri
- Shugaba Xi Ya Tattauna Da Manyan Jami’an Gudanarwar Yankunan Hong Kong Da Macao
Tun da farko, Daraktan kudi na shirin dorewar muradin karni, Alhaji Mannir Ayuba Sullubawa ya kare kasafin kudin sashen na shekara mai kamawa.
Hakazalika, ma’aikatar kula da harkokin addinai ta kare kimana Naira miliyan 205 a matsayin kudaden manyan ayyuka na shekarar 2023.
Kamar yadda bayanai suka nuna za a ware Naira Miliyan 150 domin kammala ayyukan masallatai da makarantun isilamiyya.
Kazalika, hukumar kyautata jin dadin alhazai karkashi jagorancin shugaban hukumar, Suleiman Nuhu Kuki ya kare sama da Naira Miliyan Dubu Daya.
Daga cikin adadin, an kiyasta sama da Naira Miliyan Dubu Daya domin tafiye-tafiye kasashen waje da kuma biyan ayyukan hajji.
Bugu da kari, hukumar kula da ilimi addinin Islama ta gabatar da kasafin kudi na sama da Naira Miliyan 32.
Haka kuma, hukumar shari’a ta Jihar Katsina ta kare kiyasin lissafin kudaden manyan ayyuka na kimanin Naira Miliyan 7 a gaban kwamitin kula da kasafin kudin na majalisar dokokin jihar.
Hakan ne ya nuna cewar an kammala sirin kare kasafin kudi da aka kwashe tsawon makonni biyu ana gudanarwa.