Mai yiwuwa, Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom ya goyi bayan dan takarar shugaban kasa a jamiyyar LP a zaben shugaban kasa da ke tafe.
Ortom ya kuma danganta Obi, a matsayin dan takarar shugaban kasa da zai iya tsamo Nijeriya daga cikin matsin tattalin arziki da take fuskanta.
Ya kuma yaba wa Obi, akan ziyarar da ya kai a sansanin ‘yan gudun hijira don taya su murnar zagoyowar ranar haihuwar Annabi Isa AS.
A cewar Ortom, ‘yan takarar shugaban kasa da dama sun zo jihar yakin neman zabe, amma babu daya daga cikin su da ya zabi ya ziyarci sansanin na ‘yan gudun hijrar da kuma duba irin halin da suke ciki, sai Obi.
Gwamnan ya ci gaba da cewa, zabar da Obi ya yi na kai ziyarar a sansanin na ‘yan gudun hijrar, musamman a ranar bukukuwan na Kirismatin wanda ya kamata ne ace yana gidansa a cikin iyalinsa don gudanar da bikin, a matsayina (Ortom) mai bin addinin Kiristanci, “na sa maka albarka”.
Ortom ya kara da cewa, addu’a ta a gurin ubangiji, ita ce, ubangiji ya baka nasara akan takarar ka, inda ya kara da cewa, naga alamun kana da imani da fata na gari a tare da kai kuma ina da yakini in ka samu nasara, zaka tabbatar da gaskiya da adalci wajen shugabancin kasar nan.