Yayin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyi cewa su wayar wa jama’a kai, don su fita su karɓi katin shaidar rajista, ana saura kwanaki 60 a yi zaɓen shugaban ƙasa, ta kuma jaddada cewa ba ta yin katsalandan wajen shiga harƙallar murɗe zaɓen kowane ɗan takara ko wata jam’iyya.
Da ta ke jawabi yayin ganawa da manema labarai da ƙungiyoyin kare haƙƙi, Kwamishanar INEC ta Tarayya da ke Jihar Ebonyi, Onyeka Ugochi, ta bayyana cewa ‘yan siyasa ne ke shirya maguɗin zaɓe ba hukumar zaɓe ba.
Ugochi ta ce, “amma da ya ke a wannan zaɓe mai zuwa INEC ta fito da tsauraran matakan hana maguɗin zaɓe kwata-kwata, musamman ta hanyar amfani da na’urar tantance katin ɗan takara, wato BVAS da sauran matakai, babu yadda za a yi ‘yan siyasa su ci kasuwar maguɗin zaɓe.
Daga nan ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin kare haƙƙi su tashi tsaye sosai wajen taya INEC tabbatar da ganin cewa ‘yan siyasa ba su samu wata kafar yin maguɗi ba, komai ƙanƙantar ta.
“Za mu yi dukkan abin da doka ta tanadar da abin da ya wajaba domin mu kauce wa masu so mu haɗa baki da su. Saboda hakan ba zai yiwu mu bada kai borin ‘yan siyasa ya hau ba.
“Kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin kare haƙƙi ku tashi tsaye a matsayin ku na masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe, ku taya INEC tabbatar da ganin an gudanar da sahihin zaɓe a ƙasar nan. Ku taimaka wajen tabbatar da cewa mun yi abin da doka ta wajibta mana mu yi. Kuma ku taimaka wajen hana masu maguɗi su aikata maguɗi.”
Daga nan ta sake jan kunne da gargaɗin cewa masu ƙoƙarin sayen ƙuri’u su sani duk wanda aka kama, to zai yi zaman gidan kurkuku na ahekara ɗaya.
Kwanaki 60 kenan kafin a gudanar da zaɓe, amma tuni har INEC ta jibge jami’an tsaron da su ka haɗa da sojoji, ‘yan sanda, SSS da NSCDC a dukkan ofisoshin hukumar a yankunan da ake ganin akwai barazanar tsaro.
Idan ba a manta ba, a cikin watanni biyu da su ka gabata, an banka wa ofisoshin INEC har bakwai wuta a wasu jihohi na Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas.