Majalisar Wakilai ta bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta kara wa’adin ci gaba da rajistar masu kada kuri’a da karin kwanaki 60 daga ranar 30 ga watan Yunin 2022, domin baiwa ‘yan Najeriya damar yin rajista.
Majalisar ta kuma yi kira ga hukumar da ta tura karin ma’aikata da na’urorin rajistar masu kada kuri’a a fadin kasar domin cimma wannan bukatar.
Shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan jama’a na majalisar, Honarabul Benjamin Kalu, ya yi nuni da cewa, shirin Sabon rajistar masu kada kuri’a da INEC ta shirya za a dakatar da shirin a ranar 30 ga watan Yuni, 2022, gabanin babban zabe na 2023.
Ya ce matakin dakatar da rajistar masu kada kuri’a ya yi daidai da tanadin dokar zabe ta 2022 wadda ta bukaci INEC ta dakatar da rajistar masu zabe akalla kwanaki 90 kafin zabe.
Kalu ya sanar da cewa a watan Afrilun 2022, INEC ta bayyana cewa kusan kashi 42 cikin 100 na rajistar masu kada kuri’a da aka yi rajista tun bayan fara shirin a ranar 28 ga watan Yuni, 2021, sun lalace.
Kashi 42 cikin 100 ya kai kimanin Katin zabe na dindindin (PVC) guda miliyan 20.
Benjamin ya bayyana cewa, an samu rahoton karancin na’urorin rajistar masu kada kuri’a, da rashin isassun ma’aikata a cibiyoyin rajistar.
Ya kara da cewa, sashi na 9(6) na dokar zabe ta 2022 ya bada damar yin rijistar masu kada kuri’a har zuwa kwanaki 90 gabanin babban zaben kasar.
Kakakin Majalisa, Hon. Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa tun da akwai wani tanadi a cikin dokar zabe, kiran da akayi na a tsawaita wa’adin bai karya doka ba.