Kasar Sin na kara inganta samar da magunguna daban-daban don yin rigakafi da magance kamuwa da COVID-19, bayan da kasar ta inganta matakanta na dakile yaduwar cutar.
Masana’antu da dama a faɗin kasar, suna aiki ba dare ba rana, don samar da marufin baki da hanci, na’urorin gwajin cutar, da maganin zazzabi da rage radadi, da sauransu, don tabbatar da wadatuwar kayayyakin ga masu bukata.
Haka kuma, kasar Sin ta karfafa jigilar kayayyakin jinya zuwa yankuna. Ya zuwa ranar 28 ga Disamba, sama da magungunan ibuprofen miliyan 174, da paracetamol miliyan 60 da na’urorin gwajin COVID-19 miliyan 550, aka ware zuwa muhimman wurare a fadin kasar. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp